Hijirar Manzon Allah (s) zuwa garin Madina ya bude wani sabon shafi na wannan sako na Allah, don a lokacin ne Musulunci ya fara kafuwa har ya zama ya fara yaduwa zuwa kowane bangare na kasashen Larabawa saboda samun karuwar musulmi da aka yi.
A baya dai mun nuna cewa Manzon Allah (s) yana da shekaru hamsin da uku a lokacin da ya yi wannan hijira; don haka ya zauna a garin Madina ne na tsawon shekaru goma, inda a garin ne ya kare sauran rayuwarsa da ke cike da abubuwan mamaki; don kuwa a cikin wannan lokaci ne wannan sako na Ubangiji ya kai wani matsayin na cika, kuma muhimman abubuwa suka yi ta faruwa inda daga karshe dai suka haifar da kakkarfar hanya ta yaduwar Musulunci da kuma isarsa ko ina a duniya.
Don haka a nan za mu yi dubi ne cikin manyan abubuwan da suka faru dangane da rayuwar Annabi Muhammad (s) da Musulunci a garin Madinan:
GINA MASALLACI NA FARKO
Da shiga garin Madina dai abu na farko da Annabi (s) ya yi shi ne gina masallaci, wato masallacin farko a tarihin Musulunci. Ginin wannan masallaci na daga cikin muhimman ci gaba ga musulmi wadanda yanzu suka sami matattara ta kansu inda za su rika taruwa, makaranta inda za su rika koyon karatun Alkur'ani, kana kuam cibiyar karbar umarni da hani daga shugabansu. A halin yanzu lokacin buya don tsoron cutarwa ya wuce.
A wannan lokacin dai dukkan al'ummar musulmi da suka hada da Muhajirai (Mutanen Makka da suka yi hijira) da kuma Ansar (mutanen Madina da suka tarbe su) ne suka ba da himma da dukkan karfinsu wajen gina wannan masallaci, wanda daga baya ake kiransa da Masjidun Nabi (Masallacin Annabi). An gina wannan masallaci ne da yumbu da takkan dabino don yi masa rufi. Manzon Allah (s) da kansa ya kasance cikin masu ginin wannan masallaci, inda da shekara ta zagayo ya fadada masallacin saboda karuwar da musulmi suke yi.
Bayan gina wannan masallaci dukkan musulmi cikin farin ciki sukan taru don gudanar da salloli a cikinsa karkashin jagoranci Manzon Allah (s). Bayan salla kuma ya kan gabatar da huduba, ya koyar da musulmi Alkur'ani da dokokin Musulunci; haka kuma ya kan tattauna da su, ya kan saurari matsalolinsu don samun hanyoyin da za a magance su da dai sauransu.
Don haka dai wannan masallaci ya zama helkwatar gwamnatin Musulunci ta farko wadda Manzon Allah (s) ya kafa. Har yanzu wannan masallaci na nan, ko da yake an kara fadada shi da kuma kawata shi cikin karnonin da suka wuce. A halin yanzu kuma kabarin Manzon Allah (s) a cikin wannan masallaci ya ke, inda miliyoyin musulmi daga ko ina kan kai masa ziyara kowace shekara.
KULLA 'YAN'UWANTAKA TSAKANIN MUSULMI
Abu na biyu mai matukar muhimmanci da Manzon Allah (s) ya yi bayan isarsa Madina shi ne hada 'yan'uwantaka tsakanin Muhajirai da Ansar, inda ya hada kowani Muhajiri da Ansar guda a matsayin dan'uwa.
Mai son karin bayani kan wannan kulla 'yan'uwantaka sai ya matsa nan Kulla 'Yan'uwantaka don ganin karin bayani.
MAKIRCIN KURAISHAWA BAYAN HIJIRA
Kubutar Manzo (s.a.w.a) daga hannun Kuraishawa da isarsa Madina lami lafiya sun kara tunzura Kuraishawa da sa su ci-gaba da makirce-makircensu da shirye-shiryensu na gamawa da shi. Wannan bai kasance wani boyayyen abu ba, maimakon haka shugabannin Kuraishawa sun sha fitowa fili su bayyana haka.
Kuraishawa sun ci-gaba da yi wa Musulmi bita-da-kulli na kuntatawa da cutarwa, sawa'un Muhajirai ne ko duk wanda suka san musuluntarsa a Makka. Haka sun rikewa Musulmi dukiyoyinsu da mamaye gidajensu da sauran kayayyakinsu da ke Makka.
Ta wata fuska kuma, sun kasance suna bin diddigin irin yanayin da Manzo (s.a.w.a) ke ciki, suna kwadaitar da wannan kabila ko waccan da cin zarafin Annabi da mabiyan shi. Wannan ya sa Manzon Allah daukan wasu matakai don samar da kariya ga da'awa da kiyaye shi.
Farkon matakin da Annabi (s.a.w.a) ya dauka shi ne kyautata yanayin da ke kewaye da Madina, inda ya aika da wasu tawagu, ya ja-goranci wasu zuwa kabilun da Mishrikai da ke makwabtaka da su. Wannan ya haifar da wasu yarjeniyoyin sulhu da hadin gwuiwa tare da su, don gujewa yaki da zubar da jini. A daidai lokacin kuma, Manzo (s.a.w.a) ya kasance yana daidaita yanayi a cikin Madina, yana kunce makirce makircen kafiran Kuraishawa na zaburar da mazauna wannan yanki a kan yaki da musulmi.
A wani bangaren kuma shi da kansa Manzo din (s) ya kan dauki wasu matakai na takurawa wa wadannan kafirai da kuma sanya musu takunkumi, ganin cewa su ma kafiran sun fara kwace dukiyoyin al'umman musulmi, duk wadannan matakai dai da Annabin ya dauka da nufin yin maganin kulle-kullen da kafiran suke yi na kai wa musulmi hari.
Lalle babu shakka dai irin wadannan matakai na Annabin (s) ya dauka sun yi nasara bugu da kari kuma kan cewa wadannan kabilu da suka kulla yarjejeniya da musulmi su ma sun cika alkawurran da suka yi. Don haka sai kafiran suka fara tunanin fada wa musulmin da yaki don gamawa da su.
Don haka ne ma ake cewa dukkan yakukuwan da Manzo (s) ya yi su ne a matsayin kariyar kai ba wai don tsokana ba, kamar yadda haka ke bayyane ga wanda ya karanta yanayoyinsu kamar yadda ya kamata. A kan haka Allah Madaukaki ke cewa:
An yi izini (na yin yaki) ga wadanda ake yakarsu, do an zalunce su, hakika kuma Allah Mai iko ne bisa taimakon su. (Su ne) Wadanda aka fitar daga gidajensu ba da wani laifi ba, sai don kawai sun ce: 'Ubangijinmu (shi ne) Allah'. Surar Hajji:39-40.
KARSHEN MAKIRCE-MAKIRCEN YAHUDAWA
Hakika tun lokacin da Manzon Allah (s) ya koma garin Madina, sai wadannan miyagun Yahudawa na Madina suka bijire masa da kiransa na Musulunci, kamar yadda suka nuna gaba da kiyayya ga Annabi Isa (a.s) a shekaru masu yawa da suka wuce. Wadannan makiran Yahudawa sun hada kai da mushrikan Makka don kawo karshen Musulunci; don haka ne ma suka kulla makircin kashe Manzo (s), duk kuwa da yana kyautatawa da taimakonsu don kwadaitar da su ko za su karbi wannan sako na Musulunci.
Amma ko da ya ga makirce-makirce da zaluncinsu sai ci gaba suke yi, sai ya ga ba shi da zabi face ya yake su don kare Musulunci da musulmi.
Ya yi fito na fito ne da su ne a yakin nan da ake kira Yakin Kaibara wanda bayani kansa ya wuce. A yayin wannan yaki dai Imam Ali (a.s) ya nuna jarunta kwarai da gaske, inda daga karshe dai Annabi (s) ya yi nasara akan wadannan yahudawa kuma aka kawo karshen katsalandan dinsu.
SULHUN HUDAIBIYYA
Wani muhimmin al'amari da ya faru a rayuwar Manzon Allah (s) da ci gaban sakon Musulunci shi ne Sulhun Hudaibiyya
Abin da ya faru dai shi ne: Wata rana Manzon Allah (s) ya yi mafarkin cewa shi da sahabbansa sun shiga Dakin Ka'aba a garin Makka don yin dawafi, amma kafiran Makkan suna kokarin hana su. Saboda wannan mafarki ne sai Manzo (s) ya yanke cewa zai tafi Makka shi da sauran musulmi kimanin dubu daya da dari biyar don yin aikin hajji, hakan kuwa ya faru ne a shekara ta shiga bayan hijira.
A lokacin da suka wani wuri da ake kira Hudaibiyya sai suka tarar da kafirai sun toshe duk wata hanyar shiga Makka; ganin haka sai Annabi (s) ya aike da wani manzo nasa zuwa ga kafiran don shaida musu manufar zuwansa da kuma nuna musu a shirye yake ya yi sulhu da su.
Dama Kuraishawa na fama da zafin galabarsu da aka yi a yakin Khandak; don haka da suka lura da irin karfin Manzo (s.a.w.a) da nacewarsa a kan abin da ya ke so, suka kuma riski irin raunin da suke fama da shi da gazawarsu a yaki, sai suka amsa kiran Manzo (s.a.w.a). Da haka aka rattaba hannu a kan yarjejeniyar sulhu.
Daga cikin yarjejeniyar da aka kulla har da cewa tawagar musulmi a wannan shekarar ba za ta shiga Makkan ba, maimakon haka sai ta koma shekara ta gaba da dai sauran sharuddan da aka cimma.
Saboda hakan ne sai Manzon Allah (s) da sahabbansa suka koma Madina, amma da shekara ta zagayo, sai suka dawo inda suka shiga Makkan kuma suka gudanar da wannan ibada da suke son gabatarwa. Ta haka ne dai mafarkin da Annabi(s) ya yi ya tabbata.
Wannan sulhu da aka cimma dai ya haifar da babban tasiri a tarihin ci-gaban Musulunci, yayin da ya bayar da dama ga Musulmi wajen isar da sakonsu ga wadanda ba Kuraishawa ba na daga mazauna tsibirin Larabawa, sannan suka sami sararin sabuwar gwamnatinsu da karfafa ta.
KIRAN SHUWAGABANNI ZUWA GA MUSULUNCI
Cin garin Makka da yaki da rugurguza gumaka daga Dakin Ka'aba da musulmi suka yi ba karamar nasara ba ce gare su (musulmi); don haka da kuma irin halayen kwarai da dattaku da Manzon Allah (s) ya nuna wa makiyansa bayan ya samu nasara akansu, alhali kuwa suna tunanin zai musguna musu da kuma neman daukan fansa kan abubuwan da suka masa, ya sa da dama daga cikinsu suka karbi Musulunci.
Wannan nasara dai da musulmin suka sam ya sa a halin yanzu sun kasance masu karfi, to ganin haka da kuma cewa hasken Musulunci ya kori duhun zalunci da kafirci daga mafi yawa daga cikin daular larabawa, sai Manzon Allah (s) ya ga cewa a halin yanzu ya zama wajibi a sanar da sauran daulolin duniya makwabta wannan sako na Musulunci da kuma kiransu zuwa gare shi.
Don haka sai ya aika da wasiku zuwa ga sarakunan kasashen Farisa, Rum, Habasha da sauran sarakunan kasashe da kabilu don kiransu zuwa ga shiriya da hasken Musulunci.
Koda wakilan Manzo din (s) suka isa, wasu sarakunan sun karbi Musulunci, wasu kuma sun ki amincewa amma sun yarda a yi sulhu, yayin da wasu kuma irin su sarkin Farisa, wadanda ba wai kawai sun ki amincewa da sakon ba ne, a'a har ma ya ga wasikar Manzon (s) suka yi da kuma wulakanta wakilin da ya kai musu sakon.
MUBAHALA DA KIRISTOCI
Daga cikin wasikun da Annabi (s) ya aika wa sarakuna da shugabannin kasashen don kiransu zuwa ga Musulunci har da wanda ya aika wa Kiristocin Najran da Yaman. Lokacin da suka karbi wasikarsu, wadannan ba wai kawai ma sun ki yarda da Musuluncin ba ne face ma dai sai suka yi aniyar zuwa garin Madina don kalubalantar Annabi (s) da kuma kokarin kare mummunan akidar nan tasu ta cewa Annabi Isa dan Allah ne kuma an giciye shi.
Koda isowarsu garin Madina sai Manzon Allah (s) ya gabatar musu da dalilai masu karfi daga Littafan Ubangiji da suka gabata dangane da gaskiyar Musulunci, to amma duk da haka dai sun ki yin imani. Don haka sai bangarorin biyu suka yanke shawarar haduwa a wani budadden don yi la'anceceniya da kuma rokon Allah Ya saukar da azaba akan makaryaci.
Don haka sai Allah Madaukakin Sarki ya umarci ManzonSa (s) da ya tafi da danginsa makusanta wannan wuri na la'anceceniya (Mubahala)Allah Yana cewa:
Sannan wanda ya yi jayayya da kai game da shi, bayan abin da ya zo maka na ilmi, to ka ce: Ku zo mu kira 'ya'yanmu da 'ya'yanku, da matanmu da matanku, da mu kanmu da ku kanku, sannan mu shiga yin addu'a don sanya tsinuwar Allah a kan makaryata(Surar Ali Imrana: 3:16)
Ko da lokacin ya yi, sai shugabannin wadannan kiristoci suka zo wannan wuri da jama'arsu, kana shi kuma Manzon Allah (s), a bisa umarnin Allah, sai ya zo danginsa makusanta, wato: 'Yarsa Fatima (a.s) a gaba, yana rike da jikansa Hasan a hagu, Husaini kuma a dama sannan sirikinsa kuma dan baffansa Aliyu bn Abi Talib (a.s) yana biye a baya, ya shigo wannan fili.
Hakika wadannan kiristoci dai ba su taba ganin mutane masu kwarjini irin wadannan makusantan Annabi ba. Don haka ko da shugabansu ya ga Manzo da wadannan taurari iyalai na sa, sai ya razana, ya gano cewa wallahi ba su da gaskiya kuma idan har suka bari aka yi la'anceceniya to lalle fa Allah zai la'ancesu saboda wadannan mutane. Don haka sai ya janyo mutanensa ya gaya musu cewa wallahi ya ga wadansu mutane wadanda idan da za su addu'a Allah Ya sauko da wannan dutse da ke bayansu to wallahi Allah Zai saukar da shi. Don haka sai suka ja da baya suka ki yin mubahalan, inda suka yi sulhu da Manzon Allah da kuma alkawarin za su dinga aiko da Jizya ga musulmi kowace shekara, don dai a barsu su tafi.
Mai Son Karin Bayani Kan Mubahala Yana Iya Matsa Nan.
HAJJIN BAN KWANA
A shekara ta goma bayan hijira, Manzon Allah (s) ya fito, shi da dukkan matansa da ayari mai yawa na daga sahabbansa don yin aikin hajji, hajjin da daga baya ake kira da Hajjin BanKwana.
Manzon Allah (s) ya isa garin Makka ne a ranar hudu ga watan Zul Hajji. A yayin wannan aikin hajji dai Manzon Allah (s) ya yi jawabi ga dimbin jama'ar musulmi akan Dutsen Arfa jawabin da har yau din nan yana nan a zukatan musulmi kuma zai ci gaba da zama har tashin kiyama.
A yayin wannan jawabi dai Manzo (s) bayan godiya ga Allah Madaukakin Sarki, ya yi cikakken bayani a kan dokoki da ka'idojin Musulunci, sannan kuma ya rushe duk wata al'ada ta lokacin Jahiliyya, ya kuma umarci wadanda ke gurin da su sanar da wadanda ba sa nan.
A cikin hudubar tasa ya yi magana a kan mashahurin hadisin nan na Al-Thakalain, wato fadinsa (s) cewa:
Allah Ya kira ni, kuma nan ba da dadewa ba zan amsa masa; to amma ni na bar muku wasu nauyaya guda biyu a cikinku: (su ne) Littafin Allah da Zuriyata Ahlulbaiti. Littafin Allah, igiya ce da ke hade daga sama zuwa kasa; Zuriyata kuwa su ne Ahlulbaitina. Lallai Ubangiji Mai Rahama Ya sanar da ni cewa wadannan abubuwa biyu ba za su taba rabuwa da juna ba har lokacin da za su same ni a bakin tafkin Alkausara. Ina mai gargadinku da kar ku kaurace musu.
Bayan gama wannan huduba, sai Manzon Allah (s) da tawagarsa suka kama hanyar dawowa Madina tare da dubban sahabbansa da suka rako shi zuwa wannan hajji na ban kwana.